Ƙarancin kayan koyarwa na kassara karatun yara
December 12, 2012Ƙarancin kujerun zama da kayan aiki na koyo da koyarwa na ci gaba da kassara karatun 'ya'yan talakawa a jihar Kano. Galibin dai ƙusoshin gwamnati suna kai 'ya'yansu makarantu masu zaman kansu ne, lamarin da masu fashin baƙi ke cewa wannan ne dalilin da ya sa aka kasa magance matsalolin da makarantun gwamnati ke ciki, waɗanda a kullum darajarsu ke komawa baya. Sai dai hukumomin ilimi a jihar Kano sun ce wannan matsala gadar ta suka yi kuma suna ƙoƙarin shawo kanta.
Ilimi da a hausance ake wa laƙabi da gishirin zaman duniya a kullum ƙara samun koma baya yake a jihar ta Kano, duk da kuɗaɗen da gwamnatoci ke cewa suna ware wa fannin na ilimi amma a koyaushe ba a samun wani sakamako na zahiri. Babban abin da a yanzu ke ci wa makarantun gwamnati tuwo a ƙwarya shi ne tsananin ƙarancin kayan koyo da koyarwa, musamman ma dai kujerun zama domin galibin ɗaliban makarantun firamare da na sakandare dake jihar a kan duwatsu da turɓaya suke ɗaukar darasu baya ga cunƙoson ɗalibai a cikin a ji.
Malamai da ɗalibai ke sayen kaya koyarwa
Malam Habibu Idris malamin firamare ne a jihar Kano ya bayyana irin wahalar da suke fuskanta saboda rashin kujeru da kayan aiki, in da ya ce a lokuta da dama da kuɗinsa yake sayen littattafan da ya ke amfani da su haka kuma su kansu daliban yawanci ba su da litattafai.
Sai dai kuma Alhaji Wada Doguwa shugaban hukumar ilimin firamare ta jihar Kano, ya ce bai amince da batun ƙarancin kayan aiki a makarantun ba, amma dai ya san akwai matsalar kujeru da cunkoson ɗalibai a aji.
Babangida Lamido mai fashin baƙi ne a kan al'amuran yau da kullum kuma ƙwararre a fannin ilimi ya bayyana cewar matsalar dake damun ilimi ba ta ƙarancin kayan aiki ba ce domin alfarma ta sha gaban komai a abubuwan dake gurɓata ilimi a jihar Kano.
Wani abu da shi ma ke barazana ga ilimi a jihar ta Kano shi ne yadda ake kewaye makarantu da shaguna in da ake kasuwanci, lamarin da kan rarraba hankulan dalibai. Yanzu haka ma wannan matsala ta kara tumbatsa in da wasu ke mayar da filayen makarantu suna gina shaguna, lamarin da ake zargin ko akwai haɗin baki da wasu ma'aikatan gwamnati.
Mawallafi: Nasiru Salisu Zango
Edita: Mohammad Nasiru Awal