Ƙarin takaddama kan shirin Nukiliyar Iran
March 20, 2012Rasha ta yi gargaɗin cewar Iran bata da wani zaɓi daya shige ƙera makaman Nukiliya, idan har Amurka ko Izraela suka afka mata da ƙarfin soji, akan takaddaman shirin ta na inganta sinadran Uranium. Ministan harkokin waje na Rasha Sergei Lavrov ya faɗa wa wani gidan radiyo a Moscow cewar, a yanzu haka hukumar leken asirin Amurka ta CIA da sauran jami'anta sun tabbatar da cewar basu da wata masaniya dangane da matsayin gwamnatin Iran kan sarrafa makaman Nukiliya. Sai dai acewarsa ko shakka babu, za'a cimma zartar da wanannan shawara idan har anyi yunkurin kai wa Iran din hari. Wannan bayani na ministan harkokin wajen Rasha ya zo ne, sao'i kalilan bayan gargaɗin da shugaban addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bayar na cewar, ƙasarsa na shirye wajen mayar da martani daidai da harin da Amurka ko Izraela za su kai mata.
Bayan ganawarsa da takwaransa na Izraela Ehud Barak, shima ministan harkokin tsaro na tarayyar Jamus Thomas de Maiziere ya bayyana illolin dake tattare da yunƙurin amfani da karfin soji akan Iran zai haifar da babbar illa akan Izraela dama yankin baki ɗaya.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Muhammad Nasir Awal