1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙarin tallafin kuɗi ga ƙasar Girka

June 10, 2011

Rashin agazawa ƙasar Girka da ƙarin tallafin kuɗi na iya shafar tattalin arzikin duniya inji Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble.

https://p.dw.com/p/11YHG
Ministan kuin Jamus Wolfgang SchaeubleHoto: dapd

Ministan kuɗin Jamus Wolfgang Schäuble ya faɗawa majalisar dokokin tarayya a Berlin cewa ƙasar Girka za ta buƙaci ƙarin tallafin gaggawa domin bunƙasa tattalin arzikinta. Wolfgang yace halin da ƙasar ta Girka ke ciki babban abin damuwa ne. Yana mai cewa idan ba'a samarwa ƙasar ƙarin kuɗaɗe da za ta bunƙasa kasafin kuɗinta na shekarar 2012 ba, to kuwa babu shakka hakan zai yi barazana ga cigaban tattalin arzikin duniya baki ɗaya. Ministan kuɗin na Jamus Wolfgang Schäuble yace tun da farko Girka ta sami rance daga takwarorin ƙasashe na ƙungiyar tarayyar Turai da kuma asusun bada lamuni na duniya to amma bashin zai ƙare ne a ƙarshen wannan shekarar. " An amince za'a bayar da bashin ne kashi-kashi a tsakanin watanni hurhuɗu kamar yadda ƙa'idar bashin ya tanada kuma wajibi ne ya a tabbatar da hakan ta rahoton bai ɗaya daga babban bankin tarayyar Turai da asusun bada lamuni na duniya da kuma hukumar tarayyar Turai".

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Yahouza Sadissou Madobi