Ƙasar Girka ta amince da sharaɗin da aka shinfiɗa mata na samun bashin Euro miliyan dubu 120 daga ƙungiyar EU da kuma Asusun IMF
May 2, 2010Ƙasar Girka ta Amince da sharaɗin da aka shinfiɗa mata na samun bashin Euro miliyan dubu 120 daga ƙungiyar EU da kuma Asusun bada lamani ta duniya IMF.
Firaministan Girka wanda ya bayyana hakan, yace sharuɗɗan sun haɗa da matakan tsuke bakin aljihun gwamnati dazai rage albashi ga ma'aikata da kuma 'yan fansho.
Firaministan na Girka George Papandreou a don haka yayi kira ga al'umar ƙasar dasu nuna amincewar su game da wannan sabon mataki domin ceto ƙasar daga halin da take ciki na taɓarɓarewar tattalin arziki.
A yau lahadi ne dai ministocin kuɗi na ƙasashen na Turai 16 ke ganawa a birnin Brussels a ƙarƙashin jagorancin Firaministan Luxembourg Jean-Claude Juncker domin duba irin tallafin da za'a baiwa Girkan.
Mawallafi:Babangida Jibril
Edita:Abdullahi Tanko Bala