1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro na tunanin gudanar da taron gaggawa

July 13, 2011

Ana buƙatar ɗaukar ƙwararan matakan daƙile yaɗuwar rikicin kuɗi da na tattalin arziki da kuma na basussuka a tsakanin ƙasashen na Turai.

https://p.dw.com/p/11uLx
Hoto: picture alliance/dpa

Asusun ba da lamuni na duniya IMF ya yi kira ga ƙasar Italiya da ta ɗauki sahihan matakan rage yawan basussukanta. A cikin rahotonsa na shekara akan tattalin arzikin Italiya, asusun na IMF yayi maraba da shirye shiryen gwamnati na rage yawan giɓin kasafin kuɗinta, to amma ya nuna damuwa cewa a shirin tsuke baƙin aljihun, hukumomin ƙasar sun yi kyakkyawan fata fiye da ƙima game da bunƙasar da wannan shiri zai samar. Waɗannan kalaman sun zo ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa Italiya za ta zama ƙasa ta gaba a jerin ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin Euro, da za ta fuskanci mummunan rikicin kuɗi. An kuma nuna damuwa game da ƙasar Ireland da cewa tana iya fuskantar rikicin kuɗin. A halin da ake ciki shugaban hukumar zartaswar tarayyar Turai Herman Van Rompuy ya yi kira da a ɗauki matakan hana wannan rikicin za ma ruwan dare.

"Wajibi ne shugabannin su yi hoɓasa fiye da bin manufofinsu na cikin gida. Ana buƙatar shawarwari na gaggawa game da matakan kariya da za a iya ɗauka domin daƙile yaɗuwar wannan rikici a tsakanin ƙasashe masu amfani da kuɗin Euro."

A ƙoƙarin hana wannan matsala bazuwa da neman bakin zaren warware rikicin kuɗin, ƙasashen tarayyar Turai na shirin gudanar da taron gaggawa.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu