1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙoƙarin murƙushe 'yan adawa a Masar

June 21, 2014

Kotu a Masar ta tabbatar da hukuncin kisa a kan shugaban Ƙungiyar 'yan Uwa Musulmi da kuma wasu magoya bayan ƙungiyar 182.

https://p.dw.com/p/1CNXz
Hoto: picture-alliance/dpa

Wannan dai shi ne hukuncin kisa mafi girma na baya-bayan nan da kotun ta yanke tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Morsi a shekarar da ta gabata. Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka da ke kudancin Minya ce ta yanke wannan hukunci karkashin jagorancin mai shari'a Said Youssef.

Wannan shi ne karo na biyu da kotu ke yanke wa shugaban ƙungiyar ta 'yan Uwa Musulmi Mohammed Badie hukuncin kisa tun bayan kifar da gwamnatin da aka zaɓa a ƙarƙashin ƙungiyar tasa. Kotun ta kuma wanke wasu mutane 400 da suma ake tuhumarsu tare da shugaban ƙungiyar.

Tun bayan da sojoji ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Masar ɗin na yanzu Abdel-Fatah al-Sisi suka kifar da gwamnatin Morsi, mahukuntan ƙasar ke ci gaba da ɗaukar matakan murƙushe ƙungiyar ta 'yan uwa Musulmi wadda suka saka a cikin sahun ƙungiyoyin ta'adda.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Abdourahamane Hassane