1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyar EU na fatan samun taimakon Rasha wajen tinkarar rikicin Euro

December 15, 2011

Majiyoyin diplomasiya sun rawaito cewa gwamnati a Mosko ta nuna shirin ba da gudunmawar Euro miliyan dubu goma ga asusun ceto kuɗin na Euro.

https://p.dw.com/p/13TGJ
Russian President Dmitry Medvedev (C), President of the European Council, Belgian Herman Van Rompuy (L) and European Commission President Jose Manuel Barroso (R) attend a joint press conference after Russia-EU summit in Southern Russian city of Rostov-on-Don, Russia, 01 June 2010. The EU leadership pledged to provide Russia with money to reform its judiciary and fight corruption, in the context of the modernization scheme. EPA/MIKHAIL KLIMENTYEV / RIA NOVOSTI / KREMLIN POOL
Van Rompuy, Medwedew da Barroso a taron ƙolin EU da Rasha na watan Disamban 2010Hoto: picture-alliance/dpa

Rikicin bashin da ya addabi ƙasashe masu amfani da takardun kuɗin Euro zai taka muhimmiyar rawa a taron ƙolin yini biyu tsakanin ƙungiyar Tarayyar Turai da ƙasar Rasha, wanda shugaban Rashar Dimitri Medvedev zai halarta. Majiyoyin dilomasiya sun ce gwamnati a Mosko ta nuna shirinta na ba da gudunmawar Euro miliyan dubu goma ga asusun ceto kuɗin na Euro. Daga cikin muhimman batutuwan da Rasha ke son a tattauna a gun taron shi ne na soke neman bisar shiga ƙasa musamman tsakaninta da ƙasashen tarayyar Turai. Medvedev da shugaban majalisar zartaswar EU Herman Van Rompuy na shirin cimma yarjejeniya kan matakan wucin gadi bisa manufa. Taron ba zai tattauna akan batutuwan da ake takadama kais ba wato kamar halin da ake ciki a Jojiya da Libiya da kuma matakan da gamaiyar ƙasa da ƙasa za ta iya ɗauka kan Siriya a dangane da murƙushe 'yan adawa da gwamnatin ƙasar ke yi.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu