1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ƙungiyoyin ƙodagon Girka suna wani sabon yajin aiki

June 29, 2010

Kusan komai ya tsaya cik a manyan biranen Girka sakamakon yajin aikin yini ɗaya da ma'aikatan ƙasar ke yi

https://p.dw.com/p/O5Uh
Cibiyar ƙodagon GirkaHoto: AP

Ƙungiyoyin ƙwadogon Girka sun shiga wani sabon yajin aikin gama gari domin ci gaba da Allah wadai da matakin tsuke bakin aljihu da gwamnati ta ɗauka. Bankuna da kuma makarantun ƙasar za su kasance a rufe a tsawo yini na yau Talata. Rahotannin da ke fitowa daga babban birnin ƙasar sun nunar da cewa tuni harkokin sufuri suka gurgunce a Athens da kewaye da kuma manyan biranen ƙasar.

Ma'aikata sun ƙudirin aniyar gudanar da maci a titunan Athens da kuma gaban majalisar dokoki domin nuna rashin jin daɗinsu da zabtare musu albashi da gwamanti ta yi. Koma bayan tattalin arziki da ƙasar ta Girka ta fiskanta, da kuma ya sa bashi yayi mata kanta ne ya sa ta ɗauki matakin tsumulmular kuɗi domin rage giɓin da kasafin kuɗinta ke fiskanta.

Girka ce ƙasar farko ta Turai da ke amfani da takardar kuɗin Euro da ta sami kanta cikin matsin tattalin arziki tun bayan ƙirƙiro da kuɗin.

Mawallafi: Mouhamadou Awal

Edita: Yahouza Sadissou