Ƙuri'ar raba gardama na gudana a Masar
January 14, 2014Bayan kammala gaggarimin kamfen ɗin tallata sabon kundin tsarin mulkin da yin kira ga 'yan ƙasar da su amince da kundin, dubban 'yan ƙasar, da galibinsu masu goyan bayan juyin mulkin soji, sun yi dafifi a rumfunan zaɓe. Domin kaɗa ƙuri'un amince wa da kundin da zai bai wa sabbin mahukuntan ƙasar halarcin juyin mulkin da suka yi, kamar yadda masu kira da a ƙaurace wa kaɗa ƙuri'ar ke cewar.
"Wannan zaɓe na jeka na yi ka, munufarsa ita ce gwadawa duniya cewa, akwai demokraɗiyya a Masar. Sannan akwai neman halarta juyin mulki. Lokacin da rumfunan zaɓe suka zama kamar wasu barikokin soji, yadda aka jibge fiye da rabin dakarun sojin ƙasar a cikinsu. Cikin wannan yanayin razana, akwai yancin zaɓi ke nan?"
Cikin wannan yanayin matsanancin tsaro, wasu daga cikin waɗanda suka kaɗa ƙuri'a, sun yi fatan samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar, bayan amince wa da sabon kundin;"Na kaɗa ƙuri'ar amincewa da sabon kundin. Allah Ya kwantar mana da guguwar da ke kadawa. Domin a baya, mutane da dama sun mutu. A yanzu kam, sai dai mu yi tayin addu'ar samun zaman lafiya."
Sama da mutane miliyan 50 ne dai suka cancanci kaɗa ƙuri'a da za a yi kwanaki biyu, a rumfunan zaɓe sama da dubu talatin, kafin a sanar da sakamakon.Mahukuntan ƙasar ta Masar sun ce, zaɓen na tafiya cikin lumana, amma an samu wasu matsalolin harbe-harbe tsakanin wasu 'yan ta'adda biyar da jami'an tsaro. Sannan wani bam ya tashi a farfajiyar kotun tsarin mulki, ba tare da kowa ya jikkata ba.
Ɗaruruwan masu saka ido na ciki da waje, na duba yadda zaɓen share fagen ke gudana.Jam'iyyar Mirs Qawiyya, ta ɗan takarar shugaban ƙasa, Abdul futuh, wacce ta yi niyar shiga kaɗa ƙuri'ar, ta janye daga baya, saboda abin da ta kira, tabbacin da ta ke da shi na shirya maguɗi a zaɓen. Hamdain Sabbahi, farar hula ɗaya tilo da ke shirin ƙalubalantar shugaban hafsoshin sojin ƙasar, Abdul Fatah al-Sisi, a neman shugaban ƙasa, bai sami dammar kaɗa ƙuri'ar ba, saboda rashin samun sunansa a kundin masu kaɗa ƙuri'a.
Mawallafi: Mahmud Yahya Azare
Edita: Usman Shehu Usman