Ɗan asalin Pakistan ake zargi da harin New-York
May 4, 2010Hukumomin Amirka sun tsafke wani ɗan asalin ƙasar Pakistan da ake zargi da yunƙurin kai hari kan dandalin shaƙatawa nan na Times Square da ke birnin New-York a ranar asabar da ta gabata.
Ministan shari´a na ƙasar ta Amirka, wato Eric Holder ya ce an kama wani matashi mai suna Shahzad Faisal a filin jirgin sama a lokacin da ya ke neman arcewa daga ƙasar i zuwa Dubai. Wannan matashi mai shekaru 30 da haihuwa, yana da zama ne a jihar Connecticut na arewa maso gabashin Amirka.
Tun a jiya ne hukumomin na Amirka suka fara farautan wanda ake zargi da yunƙurin ɗana bam a cikin wata mota ruwa a jallo. Ba akai ga samun alaƙa da ƙungiyar Taliban ta ƙasar Pakistan da ta yi iƙirarin kai harin da kuma shi Faisal da aka kama ba.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu