1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

2019: Yanayin zafi a duniya ya karu

Lateefa Mustapha Ja'afar
December 3, 2019

Wani kiyasi na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana shekarun 2010 zuwa 2019 a matsayin wadanda duniya ta fi fuskantar tsananin zafi a tarihi.

https://p.dw.com/p/3U98u
Spanien Madrid l  25. UN-Klimakonferenz - Logo
Taron sauyin yanayi na COP25 a Madrid na gudanaHoto: Getty Images/P. Blazquez Dominguez

Yayin babban taron sauyi ko kuma dumamar yanayi na COP25 da ke gudana a birnin Madrid na kasar Spain, majalisar ta nunar da cewa karuwar zafin na da nasaba da dumamar yanayi da kuma yadda teku ke kara tumbatsa. Rahotanni sun nunar da cewa a shekara ta 2019 da muke ciki kawai, zafin ya karu a duniya da sama da digiri daya a ma'aunin Celsius. Tun dai daga shekara ta 1850 ne, aka fara tantance yadda  yanayi yake sauyawa a duniya.