A Berlin an tattauna kan matakan da za´a dauka kan shirin nukiliyar Iran
September 8, 2006Talla
A taron da suka yi a birnin Berlin game da shirin nukiliyar Iran da ake takaddama akai, kasashe biyar masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD da kuma Jamus sun tattauna a kan matakin da za´a dauka nan gaba. To sai dai ba´a san irin ci-gaban da aka samu ba. Wani babban jami´in diplomasiya na Turai ya ce tattaunawar ta ta´allaka ne akan kudurin kwamitin sulhu mai lamba 1696, wanda yayi kira da sanyawa Iran takunkumi idan ta ki cika wa´adin ranar 31 ga watan agusta na ta dakatar da shirin inganta sinadarin uranium. Wannan dai shine taron manyan kasashen 6 na farko tun bayan cikar wannan wa´adi, wanda Iran ta yi watsi da shi. A lokacin da yake magana a birnin Atlanta shugaban Amirka GWB ya ce yanzu duniya ta hada kai don daukar matakai na bai daya akan gwamnatin Teheran. A kuma halin da ake ciki babban mai shiga tsakani na Iran a tattunawar da ake yi na nukiliya, Ali Larijani ya ce a gobe asabar zasu gana da babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana.