1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

'Yan wasan Afirka sun nuna bajinta

Mouhamadou Awal Balarabe AH
August 28, 2023

'Yan wasan Afirka sun yi ungulu da kan zabo a gasar guje-guje da tsalla ta duniya, inda suka nuna bajinta a wasu sabbin fannoni amma suka kasa cimma yawan lambobin da suka samu a baya.

https://p.dw.com/p/4VeZH
Hoto: Alain Suffo/Sports Inc/empics/picture alliance

Kungiyoyin kwallon kafa da ke wakiltar Nijar ba su samu zarafin shiga gasannin da hukumar kwallon kafar nahiyar Afirka ta gudanar a a karshen mako ba, sakamakon takunkumin da aka kakaba wa kasar biyo bayan juyin mulkin da sojojin suka yi a ranar 26 ga watan Yuli.  Dama dai a cikin wata sanarwar Fénifoot da kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya samu kopi, ta ce ta yanke shawarar ficewa daga gasar ne sakamakon illar da takunkumin da kungiyar ECOWAS ta sanya wa Jamhuriyar Nijar, wanda ke kawo cikas ga zirga-zirgar jama'a. Ya kamata dai kungiyoyi biyu da suka fito daga birnin Yamai wato AS Garde Nationale da AS Douane su fafata a wasannin share fage na gasar zakarun Afirka da kuma gasar cin kalubale na CAF. Sai dai yanayin zamantakewa siyasar a Nijar, ya sa hukumar kwallon kafar Afirka mayar da wasannin da kungiyoyin Nijar za su buga a gida zuwa wasu kasashe. Amma dai Fénifoot ta danganta wannan matakin da karin wahala ga kungiyoyinta.

An kammala zagaye na farko na gasar cin kofin zakarun Afirka

Fußball Spieler Christian Atsu
Hoto: Richard Lee/BPI/Shutterstock/IMAGO

A filayen kwallon na kasashen na Afirka dai, an kawo karshen zagayen share fage na gasar cin kofin zakarun nahiysar, inda a gida Garoua, Coton Sport ta Kamaru ta sha kashi a hannun Real Bamako ta Mali da ci 2-0, lamarin da ya sa aka sallame ta daga gasar. Ita ma Remo Stars da ke wakiltar Najeriya ta yi rashin nasara a gaban Medeama SC ta Ghana da ta cire ta a bugun daga kai sai mai tsaron gida. Amma a nata bangaren Asec Mimosas ta Abidjan ta doke Coton Sport ta Jamhuriyar Benin da ci 2-0 bayan da suka tashi 0-0 a wasan farko, yayin da Al Ahli ta Tripoli ta samu damar hayewa mataki na gaba bayan da ta lallasa Nouadhibou FC 1-0. Ita kuwa Saint George FC ta Habasha ta samu gurbin zuwa zagaye na gaba bayan da ta doke Tanzaniya KMKM da ci 3. Ita ma Big Bullets ta Malawi ta haye bayan da ta yi dragon Fc ta Eqautorial Guinea 1-0. Sai dai LISCR ta Laberiya za ta je zagaye na biyu bayan da ta yi 1-0 da Bo Rangers a wasanni duka biyu. A Bangaren gasar cin kofin kalubale na CAF kuwa, FUS Rabat ta Maroko ta ci gaba da jan zarensa inda ta doke AS Loto ta Benin da ci 2-0. Ita ma kungiyar Dreams FC ta Ghana ta yi nasara ganin badi bayan da ta lallasa Milo FC ta Guinea da ci 2-1. Ita kuwa Zanaco ta Zambia ta doke Cano Sport ta Equatorial Guinea da ci 3-0, yayin da duk da rashin nasara da ci 2-0, kungiyar Singida United ta Tanzaniya ta haye mataki na gaba. Sai dai kungiyar Kakamega Homeboyz ta Kenya ba ta buga wasan ba bayan ta sha kashi a hannun Al Hilal Benghazi na Libya da ci 4-1.

Dage gasar lig ta Najeriya fzuwa takwas ga watan Satumba 

FIFA World Cup Qualifikation | Ghana - Nigeria
Hoto: Sunday Alamba/AP/picture alliance

Daya daga cikin kwamitocin da ke kula da gasar Firimiya Lig ta Najeriya IMC ya sanar da dage fara gasar zuwa takwas ga watan Satumba mai zuwa sakamakon rashin kammala muhimman shirye-shirye da suka wajaba kafin a kai ga fara Lig na kaka ta 2023/2024. Wannan dai ba ya rasa nasaba da rashin kammala tsara sabuwar manhajar zamani da a karon farko za ta ba wa ma'abota damar kallon wasannin kai tsaye, lamarin da kuma ya haifar da banbancin ra'ayi tsakanin masu horas da kungiyoyi da magoya baya. Wakilinmu a Bauchin Yakubu Aliyu Muhammad Waziri ya duba mana wannan batu ga kuma rahoton da ya aiko mana.

Bayern Munich ta samu nasara a karo na biyu a jere inda ta mamaye Augsburg

Bundesliga Bayern München - FC Augsburg
Hoto: Leonhard Simon/REUTERS

A babban lig din kwallon kafar Jamus na Bundesliga, Bayern Munich ta samu nasara a karo na biyu a jere inda ta mamaye Augsburg da 3-1. Kuma sabon tauraronta Harry Kane ya zura kwallaye biyu a wasa da ke zama na biyu a wannan kakar wasanni. sai dai laya ba ta yi wa Yaya-karama Borussia Dortmund kyau rufi ba, domin kuwa ta tashi kunnen doki 1-1 da makwabciyarta VfL Bochum. Saboda haka ne ta rasa maki mai daraja da zai iya bata kyakkyawan matsayi a teburin Bundesliga. Hasali ma Dortmund ba ta yi koyi da taba koyi da kura-kurai da ta tafka a wasa da Köln ba. Maimakon ma kasala da 'yan wasan BvB suka nuna ya sa  Kevin Stöger na Bochum ya shammace su a minti 13 da fara wasa. Sai ma minti goma bayan dawowa hutun rabin lokaci ne Donyell Malen ya rama wa kura aniyarta.A sauran wasanni kuwa, Union Berlin ta yi wa Darmstadt dukan kawo wuka 4-1, duk da korar dan wasanta tsakiya Brenden Aaronson da alkalin wasa ya yi sakamakon keta. Kuma albarkacin wannan nasarar, Union Berlin ce ke kan gaba a teburin Bundesliga da maki shiga, yayin da Bayern Munich da Bayer Leverkusen ke biya mata baya. Hasali ma dai, Leverkusen ta doke Borussia Mönchengladbach da ci 3-0, inda dan Najeriya Victor Boniface ya ci kwallaye biyu. A yanzu haka ma dai kungiyoyi biyar na Bundesliga ne suka yi nasara a wasanni biyu na biyu a kakar wasa ta bana ciki har da Leverkusen da Bayern Munich da Union Berlin da Freiburg da Wolfsburg.

An kammala wasannin guje-guje na duniya a Budapest

Ungarn | Leichtathletik Weltmeisterschaften 2023 in Budapest | 4x400 Meter Männer | indisches Team
Hoto: Jewel Samad/AFP

A karshen mako ne aka kammala wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na duniya a birnin Budapest na kasar Hongari. Sai dai babu yabo babu fallasa ga nahiyar Afirka kasancewar 'yan wasanta sun samu gibin lambobin biyu idan aka kwanta da wasannin karshe, inda a wannan karon suka samu lambobin 26. Kuma kamar yadda aka saba 'yan tseren Kenya da Habasha ne suka sake share wa nahiyar Afirka wahaye inda suka samu lambobi 10 da 9. Su kuwa 'yan wakilan Yuganda da Botswana da Maroko sun tsira ne da lambobi bi-biyu, yayin da Burkina Faso ta yi abin kai inda a karon farko  dan wasan tsallenta Hugues Fabrice Zango ya samu lambar zinare. Abin lura a nan shi ne, 'yan wasan Afirka sun nuna bajinta a tseren dogo da matsakaicin zango, lamarin da ya sa Faith Kipyegon kafa tarihi a tseren mita 1500/5000 a gasar guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya. Sannan dan tseren Letsile Tebogo dan asalin Botswana ya taka rawar gani inda ya samu lamba daya ta azurfa a tseren mita 100, dayan kuma ta tagulla a tseren mita 200, lamarin da ya sa shi zama dan tseren Afrika na farko da ya samu lambobin yabo biyu a gasar duniya.