Carlo Ancelotti ya kafa tarihi a gasar zakarun Turai
November 3, 2022Talla
Mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Real Madrid Carlo Ancelotti ya kafa tarihi inda ya kasance koci na farko a tarihin gasar zakarun Turai ta Champions League da ya ci wasanni daya bayan daya har sau 103 bayan nasarar da kungiyarsa ta yi a jiya.
Dan asalin kasar Italiya mai shekaru 63 a duniya Carlo Ancelotti ya taba yin gwa-gwa-gwa da takwaransa Sir Alex Ferguson mai shekaru 80 a yanzu da ya samu nasara har sau 102 a wasannin na zakarun Turai kafin kungiyar da ya ke horas wa Real Madrid ta ci wasanta na karshe, lamarin da ya sa jagoran na madarar kwallo ya ciri tuta.