1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A kammala babban taro kan harkokin tsaro a birnin Munich

February 5, 2006
https://p.dw.com/p/Bv9E
A karshen babban taron kasashen duniya akan harkokin tsaro a birnin Munich dake kudancin nan Jamus, ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana Rasha a matsayin wata kawa da ya zama dole a dama da ita wajen warware matasalolin da duniya ke fuskanta. Ministan ya ba da misali da daukar mataki na bai daya akan shirin nukiliyar Iran. Kamar ministan tsaron Rasha Sergei Ivanov shi ma Steinmeier yayi kira ga Iran da ta amince da shawarar da aka bayar na sarrafa mata sinadarin uranium a cikin Rasha. Ministan ya ce hakan zai hana tabarbarewar rikicin da ake fuskanta. Shi kuwa a jawabinsa mista Ivanov gargadi yayi game da wasu sabbin hare hare na ´yan ta´adda. Inda yace duk da kokarin da gamaiyar kasa da kasa ke yi har yanzu barazanar kai irin wadannan hare hare ba ta ragu ba. Ivanov yayi kira da a kara samun hadin kai da Jamus, da KTT da kungiyar tsaro ta NATO.