1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

A karon farko Isra'ila ta bude iyakarta ta Kerem Shalom

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 17, 2023

Turkiyya ta yi kira ga Amurka da ta yi amfani da alakar da ke tsakaninta da Isra'ila domin shawo kanta ta dakatar da yakin da ta ke yi a Zirin Gaza sakamakon yadda rikicin ke kara kazancewa

https://p.dw.com/p/4aGxd
Hoto: Abed Rahim Khatib/dpa/picture alliance

A karon farko tun bayan barkewar yakin Gaza, Isra'ila ta bude iyakarta ta Kerem Shalom a Lahadin nan, don ba da damar shiga da kayan agaji da suka hada abinci da magunguna yankin Zirin Gaza.

Wasu majiyoyi guda biyu na kungiyar agaji ta Red Crescent a Masar sun tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa manyan motocin dakon kaya guda 79 sun tsallaka iyakar, a kan hanyarsu ta isa Gaza.

Karin bayani: Wa zai sake gina yankin Gaza bayan yaki?

Iyakar ta Kerem Shalom ta hada Masar da Isra'ila da kuma Zirin Gaza, kuma an rufe ta ne tun bayan harin da kungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata, wanda shi ne ya sabbaba yakin da yanzu ya haura watanni biyu ana gwabzawa.

Turkiyya ta yi kira ga Amurka da ta yi amfani da alakar da ke tsakaninta da Isra'ila domin shawo kanta ta dakatar da yakin da ta ke yi a Zirin Gaza sakamakon yadda rikicin ke kara kazancewa.

Ministan harkokin wajen Turkiyya Hakan Fidan ne ya yi wannan kira, lokacin ya ke tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Amurka Antony Blinken a Lahadin nan, yana mai cewar bayan tsagaitar wutar, to akwai bukatar tattaunawa da Isra'ila a kan teburin sulhu wajen ganin an samar da kasashe biyu masu 'yanci, wato Isra'ila da Falasdinu.

Karin bayani:Jakadun MDD sun kadu da abin da suka gani a Rafah

Haka zalika ministocin biyu sun tattauna batun cinikin jirgin sama na yaki daga Amurka, da kuma shirin bai wa Sweden damar shiga kungiyar tsaro ta NATO, da majalisar dokokin Turkiyyar ba ta kai ga amincewa da shi ba har yanzu.