1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin bam a kasar Siriya ya hallaka gwamman sojoji

Binta Aliyu Zurmi
October 13, 2022

Wani harin bam ya yi sanadiyar salwanta rayukan sojojin kasar 18 yayin da wasu 27 suka jikkata, jim kadan bayan da bam din ya tarwatse a wata mota kirar bus a kusa da Damascus babbar birnin kasar Siriya.

https://p.dw.com/p/4I9Ob
Libanon Bombenanschlag ehemaliger Premierminister Rafik Hariri getötet
Hoto: AP

Kamfanin dillancin labaran kasar na SANA ya bayyana cewa harin na yau na zama irin shi mafi muni a kan jami'an tsoro a yan baya-bayan nan.

Yawaitar kai hari a kan jami'an tsaron Siriya da ta shafe shekaru tana fama da yakin basasa na kuruwa, kuma ana zargin mayakann jihadi da aikata shi duk da cewar har yanzu babu wanda ya dauki alhakin harin.

A watan Yunin da ya gabata wani makamancin wannan harin ya hallaka sojojin kasar 13 a yankin Raqqa da ke arewacin kasar. 

Rikicin kasar ta Siriya da ya fara a shekarar 2011 ya yi sanadiyar rayukan dubban mutane, yayin da sama da mutum miliyan biyu ne ya raba da matsugunnansu