1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A ranar 16 ga wata za a ɗage dokar ta ɓaci a Pakistan

November 30, 2007
https://p.dw.com/p/CUzI

Sakamakon matsin lamba a cikin gida da kuma daga ƙetare shugaban Pakistan Pervez Musharraf ya ba da sanarwar cewa a ranar 16 ga watan desamba zai ɗage dokar ta ɓaci da ya kafa. A cikin wani jawabi da ya yiwa al´umar ƙasar shugaba Musharraf ya ce za´a kuma sake maido da kundin tsarin mulkin ƙasar. A ranar 3 ga watan nuwamnba da ya gabata shugaban ya kafa dokar ta ɓacin bisa dalilan barazanar da ake fuskanta na ƙaruwar masu tsattsauran ra´ayin Islama. Musharraf ya yi kira ga dukkan jam´iyun siyasa da su shiga cikin zaɓen gama gari da zai gudana a ranar takwas ga watan janeru mai zuwa. Da farko shugabannin ´yan adawa wato Benazir Bhutto da Nawaz Shariff sun yi barazanar ƙauracewa zaben saboda dokar ta bacin. A jiya dai ne aka rantsad da shugaba Musharraf don sabon wa´adi na mulki.