1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau Bush zai ƙarasa Kuwaiti a ci-gaba da ziyarar ƙasahen Gabas Ta Tsakiya

January 11, 2008
https://p.dw.com/p/Co3d

A ci-gaba da rangadin da yake kaiwa ƙasashen yankin Gabasa Ta Tsakiya a yau juma´a shugaban Amirka George W Bush zai je ƙasar Kuwaiti. Kafin ya tashi daga Isra´ila Bush zai yi balaguro a wasu yankuna masu tsarki da aka ambata a cikin littafin Bible, sannan zai gana da wakilin ɓangarorin nan huɗu dake shawarta batun zaman lafiya Gabas Ta tsakiya wato tsohon Firaministan Birtaniya Tony Blair. Blair dai yana mayar da hankalinsa musammman akan bawa Palasɗinawa taimakon tattalin arziki. Bayan ganawarsu a jiya da shugaban Palasɗinawa Mahmud Abbas a yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan, shugaba Bush ya ce ya na da tabbacin cewa Isra´ila da Palasɗinawa zasu sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya kafin ya kammala wa´adin mulkinsa a cikin watan Janerun shekara ta 2009.