1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

A yau kotu a Spain zata yanke hukunci kan yan hari na Madrid

October 31, 2007
https://p.dw.com/p/C15M

A yau kotun yaki da taadanci ta kasar Spain zata yanke hukunci kan wasu mutane 28 da ake zargi da kai harin bam a cikin jiragen kasa a birnin Madrid a 2004,inda mutane kusan 200 suka rasa rayukansu.kowanne daga cikin wadannan mutane dai yana fuskantar daurin shekaru 40.Harin dai shine mafi muni tun harin ranar11 ga watan satumba na Amurka.Wadanda ake zargin dai sun musa zargin dake cewa suna da alaka da kungiyar Al Qaeda ko wata kungiya ta islama mai tsatsauran raayi.Kungiyar dai ta Alqaeda ta fito da wata sanarwa ta bidiyo kwanaki biyu bayan harin tana mai ikrarin cewa itace ta kai harin.Makonni uku kuma bayan harin wasu yan kunar bakin wake suka dana bam dake jikinsu a lokacinda yan sanda suke kokarin kama su.