A yauhugaban EU zai mika tayin ihsani ga Iran
June 6, 2006Babban jamiin hulda da wajen Kungiyar Taraiyar Turai,Javier Solana fara tattaunawa da babban mai shiga tsakani Ali Larijani a birnin Tehran na kasar Iran,inda zai mika tayin ihsani ga kasar ta Iran domin ta dakatar da shirinta na nukiliya.
Kasashen Jamus,Burtaniya da Faransa suka shawarta bada wannan ihsani,wanda ya samu goyon bayan kasashen Amurka Rasha da kuma Sin.
Ana sa ran cewa tayin da Solana zai mikawa shugannin na Iran zai hada da baiwa Iran damar sayen bangarorin jiragen sama daga kanfanin Boein da airbus.
Hakazalika ana sa ran zasu hada kuma da tayin janye takunkumin cinikaiya domin baiwa Iran damar inganta harkokin zirga zirgan jiragen samanta gami da samar mata da fasaharnoma na zamani daga Amurka.
Babu kuma wata barazanar daukar matakin soji akan kasar ta Iran idan har taki amincewa da wannan tayi.