Amirka na son warware rikicin Nijar ta fuskar diflomasiyya
August 8, 2023Babbnan sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken, ya bayyana muhimmanci da ke da akwai na amfani da diflomasiyya wajen warware takaddamar da ta barke a Nijar tun bayan kifar da Gwamnatin Bazoum.
A cikin wata hira da ta gidan rediyon Faransa, Mista Blinken ya ce Amurka na goyoyn bayan matakan da kungiyar Ecowas ke shirin dauka na bin tafarkin diflomasiyya wajen warware rikicin domin dawo da kasar kan tafarkin dimkradiyya.
Wannan dai na zuwa a yayin da ake dakon wani taron koli na gaggawa da shugabannin kasashe membobin kungiyar ke shirin gudanarwa a wannan Alhamis, da zummar mayar da hankali kan mataki na gaba da kungiyar za ta dauka kan Nijar, bayan cikar wa'adin mako guda da kungiyar ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki da su gaggauta kwance damara.
Batun amfani da karfin soja wajen dawo da hambararen shugaban kasar Nijar dai na ci gaba da rarraba kawunan bangarori da dama na Afirka da kasashen yammacin duniya.