Taron yaki da gurgusowar hamada
May 10, 2022Shugaban kasar Côte d'Ivoire kuma mai masaukin baki Alassanne Ouattara ya aza harsashin samar da kudi dala biliyan daya da miliyan 500, domin fara wani gagarumin shirin samar da abinci da farfado da gandun daji nan da shekaru biyar masu zuwa.
Shugaba Ouattara ya bayyana haka ne yayin bude taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 15 wato Cop 15 kan sauyin yanayi a Abidjan babban birnin kasar, inda ya ce shirin zai yi amfani da fasahohi kamar na jirage marasa matuka wajen shuka bishiyoyi da kuma amfani da iri mai jure fari domin gyara kasa.
A wannan makon aka bude babban taron shirin yaki da gurgusowar hamada a duniya karo na 15 a taron da aka yi wa lakabi da COP 15 a birnin Abidjan. Taron wanda zai dauki kwanaki goma sha daya ana yin sa, zai yi nazarin girmar matsalar gurgusowar hamada a duniya da kuma hanyoyin tunkararta. Jamhuriyar Nijar na daga cikin jerin kasashen duniya da ke fama da wannan matsala ta gurgusowar hamada.
Alkalumma kididdiga na gwamnatin kasar ta Nijar, sun tabbatar da cewa kaso daya daga cikin uku na kasar Nijar mai fadi murabba’in kilomita miliyan daya da dubu 267 mamayar hamada ne. Matsalolin gurgusowar hamadar na da nasaba ne da karancin ruwan sama, zaizayewar kasa, karancin itatuwa da sauyin yanayi da tsananin zafin rana da sauransu.
Nijar ta aika da babbar tawaga a karkashin jagorancin shugaban kasa Mohamed Bazoum a taron na birnin Abidjan kan yaki da gurgusowar hamada a duniya inda za ta gabatar da fasahohi na yaki da gurgusowar hamada a kasar.
Taron na COP 15 zai hada kan shugabannin duniya har tsawon makonni biyu, domin tattauna dabarun magance lalacewar kasa da sare itatuwa da gurgusowar hamada da ke haifar da fatara da karancin abinci da rikici a duniya wanda ya shafi rayuwar mutane fiye da miliyan uku.