SiyasaHabasha
Yunwa ba ta kashe mutane a Habasha
February 6, 2024Talla
Kalaman Firaminista Abiy Ahmed da ya yi ga majalisar dokoki, na zuwa ne biyo bayan gargadin da aka yi na cewa za a iya samun karuwar mutanen da ke fama da karancin abinci a kasar da ke zaman ta biyu mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka. Ya dai shaidawa majalisar dokokin kasar tasa cewa: "Babu wasu mutane da ke mutuwa saboda yunwa a Habasha," yayin da yake amsa tambayoyinsu. Koda yake, ya amince da cewa za a iya samun wadanda suka mutu saboda cututtuka da ke da nasaba da rashin abinci mai gina jiki. Habashan dai na fama da matsalolin karancin abinci da rikicin cikin gida, baya ga bala'in sauyin yanayi.