Abrini ya ce ya na da hannu harin Brussels
April 9, 2016Talla
Mutumin mai suna Mohamed Abrini ya shaidawa hukumomi a Belguium din cewar shi ne mutum nan da ke tare da wasu mutum biyu da suka kai harin kunar bakin wake a filin jirgin saman wanda ya yi sanadin rasuwar mutane da dama.
Mai magana da yawun babban mai gabatar da karar ta Belgiyam ya ce Mr. Abrini ya amince cewar ya na da hannu a harin bayan da aka nuna masa hoton bidiyon da ya ke ciki sanye da malafa kana ya na tura wasu akwatuna jim kadan kafin kai harin.