1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

2021: Abubuwan da Jamsu ta sa a gaba

January 5, 2021

Neman wanda zai maye gurbin shugabar gwamnati Angela Merkel da kuma cin nasara a yaki da annobar COVID-19 a Jamus, na daga cikin abubuwan da za a tunkara a 2021 a kasar.

https://p.dw.com/p/3nWg7
Deutschland Neujahransprache der Kanzlerin | Angela Merkel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela MerkelHoto: Markus Schreiber/REUTERS

Daga cikin abubuwan da al'ummar Jamus da ma hukumomin kasar ke son aiwatar wa a wannan sabuwar shekara ta 2021, sun hadar da al'amuran siyasa musamman ma zaben da za a yi a wasu jihohi. Abu mafi muhimmanci da al'ummar Jamus da ma wadanda ke rike da madafun iko suka fi fata shi ne, ganin an kawo karshen irin mamayar da annobar coronavirus ke ci gaba da yi a sassan kasar musamman ma idan aka yi la'akari da irin kokari da hukumomi suke yi na sanya dokokin da su takaita yaduwar cutar tsakanin al'umma. Baya ga dokokin da ke kasa, shugabannin  na ci gaba da fadakar da al'umma wajen ganin sun yi abin da ya dace da nufin cimma nasarar da aka sanya a gaba.

Karin Bayani:Coronavirus ce bala'in karni inji Angela Merkel

Merkel din dai na son al'umma su dafawa gwamnati wajen ganin sun rage cudanya da juna da nufin takaita adadin masu kamuwa da corona din wadda ta kashe gwamman mutane a kasar. Baya ga batun cin nasara a yakin da aka shiga da corona, wani abu har wa yau da ke gaban Jamusawa a wannan sabuwar shekarar shi ne, maye gurbin shugabar gwamnati da wa'adinta ke gab da karewa. Tuni dai masu zawarcin kujerar suka fara yaki ta karkashin kasa domin ganin sun samu karbuwa a wajen masu ruwa da tsaki a jam'iyyar CDU da ke cikin kawancen jam'iyyu masu mulki da ma sauran jam'iyyu da suke son su karbe madafun iko daga CDU din.

Deutschland München | Sondersitzung Kabinett | Markus Söder
Shugaban jam'iyyar CSU Markus Söder da ke kawance da jam'iyyar CDU ta Angela MerkelHoto: Matthias Balk/dpa/picture alliance

Wannan fargaba ta amshe iko daga hannun CDU ne ma ya sanya shugaban CSU da ke kawance da CDU din Markus Söder wanda shi ma ke cikin masu zawarcin kujerar shugabar gwamnatin yin gargadi ga magoya bayansu, inda ya ce lamarin fa ba zai musu kyau ba in har suka yi sake iko a kubuce musu: "Wasu na tunanin abin zai yi kyau, a ganina ya kamata a yi hattara domin kada a karshe a wayi gari da kawance na masu iko tsakanin jam'iyyar Greens ta masu rajin kare muhalli da ta SPD da kuma Die Linke da ke da ra'ayin mazan jiya."

Karin Bayani: Merkel na fuskantar gagarumin kalubale

A hannu guda kuma wasu 'yan kasar na cewa za su yi kewarta idan ta sauka daga mulki, musamman ma irin jajircewarta wajen aiki da kuma irin kokarinta na ganin an yi abin da ya dace da ma sanya kimiyya cikin siyasa. Ko da yake matsayinta kan karbar baki da ma rungumarsu hannu bibiyu ta haifar da rarrabuwar kawuna da ma bayar da dama ga jam'iyyar nan ta AfD mai kymar baki, samun kujeru a majalisar tarayya da ta jihohi. Yanzu haka dai al'ummar Tarayyar Jamus din, na zuba idanu kan irin yadda al'amura za su wakana a wannan shekara ta 2021, shekarar da mafi akasarin 'yan kasar ke cike da fata na samun sauyi daga irin kalubalen da aka fuskata a shekarar 2020 da ta gabata.