Bakin haure sun shiga Turai ta barauniyar hanya
August 12, 2022Talla
Hukumar da ke tsaron iyakokin Turai ta ce adadin mutanen da suka shiga nahiyar ta barauniyar hanya daga farkon wannan shekara zuwa ya haura da 155 000, adadin da ya kasance mafi yawa idan aka kwatanta shi da na shekarar da ta gabata.
Hukukar Frontex ta ce galibin wadanda suka keta nahiyar Turai bakin haure ne daga kasashen Siriya da Afghanistan da Turkiyya, kana kuma ko kadan alkaluman ba su shafi miliyoyin 'yan gudun hijirar Ukraine da suka kauracewa yaki ba.
Sai dai an samu karancin wadanda ke shiga nahiyar Turai daga gabashinta da kaso 32%, sabanin yadda 'ya 'yan wasu kasashe ciki har da Najeriya da Kwango suka yi kaurin suna.