Adadin 'yan gudun hijira ya karu a duniya
June 20, 2016Talla
Wani rahoto da hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya wato ta wallafa a wannan Litinin din albarkacin ranar 'yan gudun hijira ta duniya ya nunar da cewa adadin mutanen da suka bar muhallansu a dalilin yaki ko wata tsangwama a duniya a shekara ta 2015 ya kai adadin da ba a taba samu ba a tarihi inda ya kai miliyan 65 da dubu dari uku.
Hukumar ta ce tun soma yaki a Siriya a shekara ta 2011 adadin 'yan gudun hijirar na karuwa ne a ko wace shekara bayan kuwa sai da ya daina karuwa tsakanin shekara ta 1996 zuwa ta 2011. A takaice idan aka kwatanta da shekara ta 2014 to adadin 'yan gudun hijirar ya karu da kashi 9,7% a shekara ta 2015: