1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamus: Gangamin adawa da matakan dakile corona

Abdoulaye Mamane Amadou
March 20, 2021

Masu gangamin adawa da matakan kariyar da ake dauka don dakile yaduwar annobar Corona a Jamus sun yi arangama a wannan Asabar da jami'an 'yan sanda a birnin Cassel da ke yankin tsakiyar kasar.

https://p.dw.com/p/3qupb
Deutschland Gewalt bei Demo gegen Corona-Maßnahmen in Kassel
Hoto: Thilo Schmuelgen/REUTERS

Rahotanni sun ce wannan shi ne karo na biyu kenan da ake ganin tururuwar masu zanga-zangar, inda dubbam mutanen suka yi cincirindo ba tare da sun saka matakan kariya ba, kafin daga bisani jami'an tsaro su yi amfani da hayaki mai sa kwalla su tarwatsa su.

Birane da dama na tarayyar Jamus sun fuskanci zanga-zangar adawa da matakan kulle, to amma sai dai rahotanni na cewar irin wadda ta faru a Kassel na daya daga cikin mafiya muni.

Wannan lamarin dai na zuwa ne a ya yinda ko a yau din nan hukumar kula da yaduwar cututtukan kasar ta Robert Koch, ta sanar da sababin kamuwar cutar corona 16000, a yayin da wasu fiye da 200 suka rigamu gidan gaskiya.