Adamwa da OSCE a Ukraine
July 23, 2015Akalla wasu mutane 300 sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da Hukumar da ke kula da tsaro da hadin kan Turai ta OSCE, a can a yankin gabashin Ukraine. Masu zanga-zangar dai sun kewaye wani otel ne, kuma hukumar ta ce wani yunkuri ne na hana su yin aiki yadda ya kamata. Mutanen wadanda yawancinsu mata ne, sun iso otel din ne a cikin wasu motoci kirar bus, tare da rakiyar daya daga cikin jagororin 'yan aware. Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa sun yi amfani da fenti wajen rubuta sakonnin zaman lafiya da kwanciyar hankali a motocin ma'aikatan hukumar ta OSCE.
Ko da shi ke dai, a cewar hukumar, mutanen na nuna adawa da aikin da suke yi da ma kissan fararen hula ne da kuma ma yawaitan hare-hare duk da cewa akwai yarjejeniyar tsagaita wuta.
A makon da ya gabata kadai mutane fiye da 40 suka hallaka, kuma ana kiyasin mutane 6500 suka mutu tun da aka fara rikicin.