1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar adawa da sojojin Faransa

Ramatu Garba Baba LMJ
January 20, 2023

Dubun-dubatar 'yan Burkina Faso sun gudanar da gagarumar zanga-zanga, domin nuna adawarsu da kasancewar sojojin Faransa a kasar da kuma bukatar su gaggauta ficewa.

https://p.dw.com/p/4MWRH
Hoto: BOUREIMA HAMA/AFP/Getty Images

Masu zanga-zangara Ouagadougou babban birnin kasar Burkina Fason, sun yi kira ga Faransa da ta gaggauta kwashe sojojinta daga cikin kasar. Wasu daga cikinsu sun yi ta kona tutocin Faransan, yayin da wasu kuma suka yi yunkurin kutsa kai ginin ofishin jakadancin kasar da ke Ouagadougou kafin jami'an tsaro su dakile su.

Tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Augustan bara, aka samu tsamin dangantaka a tsakanin gwamnatin rikon kwaryar soja ta Burkina Fason da tsohuwar uwargijiyarta. 'Yan kasar da dama kuma na danganta tsananin hare-haren baya-bayan nan da mayakan jihadi ke kai wa da bakin jinin Faransa a wurin 'yan ta'addan, wadanda suka hana zaman lafiya a kasashen yankin Sahel. A makon da ya gabata ma dai, mayakan sun sace mutane kimanin 60 ciki har da mata da kananan yara.