1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rikici a Kwango ya kashe mutum 15

Ramatu Garba Baba
July 27, 2022

Jami'an wanzar da zaman lafiya na MDD uku na daga cikin mutum 15 da suka mutu a rikicin adawa da kasancewar dakarun MONUSCO a Kwango.

https://p.dw.com/p/4Ej9Y
Demokratische Republik Kongo | Sake, bei Goma | Proteste gegen UN
Gangamin adawa da MDDHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Zanga-zangar da ta rikide zuwa tarzoma ta soma ne bisa zargin da 'yan kasar ke wa dakarun majalisar na gazawa wajen kare rayukan fararen hula daga masu gwagwarmaya da makamai. Ramatu Garba Baba nada karin bayani a wannan rahoton da ta hada mana.

Kwanaki biyu aka kwashe ana fama da tashe-tashen hankula a Jamhuriyyar Dimukuradiyyar Kwango, tashin hankalin da ya janyo asarar rayuka goma sha biyar, uku daga ciki suka kasance jami'an da aka tsugunar don wanzar da zaman lafiya a kasar da dama rikici ya riga ya daidaita. 

A wannan karon masu zanga-zangar sun fusata ne inda suka nemi lallai, rundunar (MONUSCO) ta fice daga cikin kasar, suna masu cewa, zamansu ba shi da wani amfani ganin yadda masu gwagwarmaya da makamai ke cin karensu ba babbaka a kai hare-haren da ke lakume rayukan fararen hula dama dukiyarsu.

Sojojin kiyaye zaman lafiya na ​​MDD
Sojojin kiyaye zaman lafiya na ​​MDDHoto: Djaffar Sabiti/REUTERS

Amma ga kakakin Majalisar Dinkin Duniya a yankin Farhan Haq ya ce, zargin ba shi da tushe don kuwa dakarun na iya kokari, inda har ya kwatanta lamarin da cewa danbu ne da idan yayi yawa baya jin mai.

''Mun jima muna iya kokarinmu, shekara da shekaru muka kwashe muna kokarin samar da zaman lafiya mai dorewa a yankin gabashin Kwangon, yankin da ake da 'yan tawaye dabam-dabam da ke adawa da juna, akwai lokacin da matsi ke saka su ajiye makamansu amma sai a ga sun sake dawowa da karfinsu, duk da haka bamu taba yin kasa a gwiwa ba, mun ci gaba da yin  iya kokarinmu don ganin mun samar da zaman lafiya a gabashin Kwangon''.

Baya ga asarar rayuka goma sha biyar da aka tafka wasu sama da hamsin sun ji munanan rauni a sakamakon tarzomar kuma Janar Ndima Constant  wani jami'in soja a kasar ya danganta rikicin da ya barke da kalaman wani wakilin MONUSCO da ya fito fili ya baiyana karfin ikon Kungiyar M23 mai gwagwarmaya da makamai wanda ake ganin shi ya tunzura jama'a.

Janar Constant ya ce ''A tunanina, kalaman kakakin MONUSCO ne ya tayar da kurar amma muna kokarin lalubo mafita, abin lura a nan shi ne gwamnatin Kwango ce ta bukaci taimakon rundunar Monusco amma kuma 'yan kasa nada 'yancin fada wa gwamnati duk wani mataki da suke son ganin ta dauka''.

Masu zanga zanagar adawa da MONUSCO a Kwango
Masu gangamin adawa da MONUSCO a KwangoHoto: Moses Sawasawa/AP Photo/picture alliance

Shekaru kusan ashirin kenan da jibge dakarun na MONUSCO a gabashin Kwangon inda zarge-zarge na cin zarafin jama'a suka dabaibaye rundunar da aka tsugunar da nufin kare rayuka amma ake ci gaba da zarginta da gazawa, wasu ma na ganin tura ce ta kai bango har ake son su fice,  Har wa yau kakakin majalisar  Farhan Haq ya ce, akwai bukatar kai zuciya nesa.

''Ina kira ga mahukuntan Kwangon da kungiyoyin farar hula da sauran al'umma da su yi tir da wannan aika-aika, don bada rudani ko sabanin ra'ayoyi da rabuwar kawuna ba ne, za a samu ci gaba a kokarin da ake na ganin an samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali''.

Rigingimun kungiyoyin 'yan tawaye a gabashin Kwangon a watannin baya-bayan nan dai, sun janyo asarar rayuka baya ga tilasta wa dubbai rasa matsuguninsu duk kuwa da dokar ta baccin da gwamnati ta aiyana da kuma kasancewar dakarun nan MONUSCOn.