1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawar al'umar Girka da tsuke bakin aljihun gwamnati

October 28, 2011

Al'umar Girka sun sake gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da karin matakan tsuke bakin aljihun gwamnati

https://p.dw.com/p/131Js
'Yan zanga-zanga a GirkaHoto: dapd

Dubun dubatan jama'a sun shiga zanga-zanga a titunan biranen kasar Girka domin nuna rashin amincewarsu da matakan tsuke bakin aljihun gweamnati. Sai da ma yan zanga-zangar suka yi nasarar dakatar da faretin da sojoji ke shirin yi a garin Thessaloniki da ke gabar tekun kasar inda suka ta jefan yan siyasa da kwalabe da kwai tare da tilasta wa shugaban kasar komawa gida. Dubu dubatan jama'a ne kuma suka yi jerin gwano domin kashe kwarkwatars idonsu akan faretin da sojoji ke yi a kowace shekara domin tunawa da shigan kasar ta Girka yakin duniya na biyu. A cikin wani mataki na kin jinin Jamus wasu 'yan zanga-zangar sun ta kona tutar Jamus a lokacin da wasu kuma ke ta rera taken adawa da da ita tare da rike tutocin masu dauke da alamun yan NAZI.

Mawallafiya:Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahouza Sadissou Madobi