1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Adawar Turkiyya da bai wa Kurdawa makamai

May 10, 2017

Gwamnatin kasar Turkiyya ta sake jaddada adawarta kan matsayin Amirka dangane da wadata mayakan Kurdawa na YPG da makamai a Syria, tana mai bayyana hakan a matsayin barazana ce a gareta.

https://p.dw.com/p/2ckEd
Türkei Referendum Präsident Erdogan
Hoto: Reuters/M. Sezer

A ranar Talata ne shugaban Amirka Donald Trump ya amince da samar wa mayakan Kurdawa makamai don zafafa hare-hare kan mayakan IS a kokarin kwato birnin Raqqa a Syria.

Gwamnatin Turkiyya dai ta jima tana bayyana mayakan na YPG a matsayin 'yan ta'adda, inda ministan harkokin wajen kasar ke cewa kamata ya yi Amirka ta bambanta tsakanin dakarun Syrian Democratic Forces na larabawa da bangaren na kurdawa.

Kasar na fargabar yiwuwar mayakan na YPG su afka mata daga arewacin Syria, lamarin da ke iya ta'azzara tarzomar cikin gida da take fama da ita na tsawon lokaci.