Ado da takunkumi a kasashen Afirka
Wa ya ce sai an sarrafa kyallayen rufe baki? A Afirka wasu teloli sun tsara kellayen a matsayin sakonnin yaki da annobar coronavirus - inda suke karfafa shi da kuma barin mutane su nuna irin basirarsu.
Kyallayen rufe hanci na da daraja
Mounia Lazali, mai sana'ar dinka kayan ado a in Algeria, ya dinka daruruwan takunkumi kyauta ga jama'a – Mawakiya Joe Batoury ta yi ado da nata. Ta cewa DW "mutane na yin kwalliya da komai, don haka ba za a bar mu a baya ba mu ma. Musamman idan hakan zai karfafa wa mutane gwiwa wajen kare kansu da kansu, sana'ar tamu za ta samu karbuwa sosai a kokarin janyo hakulan mutane kullum.''
Kokarin wadatar Rwanda da takunkumi
Nshimiyimana (na biyu daga hagu) tela a Rwanda, ya tabbatarwa da DW cewa ya maida hankali kan dinka takunkumi kala-kala saboda karancinsu a kasar. Nshimiyimana na kokarin sanya farashi mai sauki ga jama'a saboda halin rayuwa kana kowa ya samu dama siya.Yana sayar da duk guda a kan dala 2 da rabi, wadanda ake sayarwa a kantuna kuma ana samun su dala a kan dala 2 kacal.
Nau'ikan kaloli mabanbanta a Laberiya
Masana'antar dinka kayan kwalliya da ke Laberiya wato Bombchel na taimakawa ma'aikata mata su tsaya da kafarsu ta hanyar basu horo wajen dinkin kayan mata. Ana amfani da wasu kayan a dinka takunkumi kamar yadda aka gani a hoton wannan matar da ke sama. Idan aka sayi guda sai a bada kyautar daya ga wanda ba zai iya zama a gida.
Takunkumi mai daukar ido a Kenya
Mai sana'ar dinkin kayan kwalliya a Kenya David Avido da ya kirkiri salon sunan nan na ''looklike avido'', ya sanya takunkumi da ya dinka da kansa, wanda ya samar daga ragowar kayan da aka dinka.Tun farkon bullar coronavirus a Kenya a watan Maris, ya dinka takunkumi fiye da dubu 10 kyauta ga jama'ar unguwannin cikin kwaryar birnin Nairobi.
Ya, da kanwa gwanyen ado a Kamaru
Ange Goufack (a bangaren hagu) da kanwarta Edmonde Kennang (a bangaren dama) suna dinka kyallayen rufe hanci masu ban sha'awa a Kamaru, su rike shi da roba ta gafe da gefe. Tun 13 ga watan Afrilu, gwamnati ta maida sanya takunkumin na hanci doka a kan kowa kafin fita bainar jama'a domin rage yaduwar cutar.
Tallafin takunkumi ga Asibitoci a Tunisiya
A lokacin da coronavirus ta bulla a kan tuntubi mai sana'ar dinka kayan kwalliya ta Tunisiya Myriam Riza a cibiyarta na Miss Anais label daga asibitoci masu fama da karancin takunkumi kan ko za ta iya samar da su. Tana samar da takunkumi ne ta hanyar dinka su daga kayan tallafi kuma tana ba da su ne a matsayin tallafi. Domin rage wannan nauyi, yanzu haka Riza na sayarwa abokan huldarta.