1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AFCON: Masar ta tsaurara matakan tsaro

Ahmed Salisu
June 21, 2019

Hukumomi a kasar Masar sun ce za su yi amfani da irin jiragen nan marasa matuka don yin sintiri a biranen da za a yi gasar cin kofin kwallon kasashen Afirka wato AFCON wadda kasar ke daukar bakunci.

https://p.dw.com/p/3KrIO
Cairo International Stadium
Hoto: picture-alliance/empics/BackpagePix

Mukaddashin shugaban hukumar kula da wasan kwallon kafar Masar Ahmed Shoubier ne ya tabbatar da hakan inda ya kara da cewar za a yi amfani ne da jiragen ne a dukannin filayen wasanni don tabbatar da tsaro yayin gasar.

Wannan dai shi ne karo farko da za a dauki irin wannan matakin a gasar ta cin kofin na kasashen Afirka. Nan gaba kadan ne kuma za a fara gasar inda za a yi wasan farko inda mai masaukin baki wato Masar za ta taka leda kasar Zimbabuwe.