AFCON: 'Yan wasan Afirka da kulob-kulob dinsu na Bundesliga za su yi kewarsu
Tun daga kan Aubameyang zuwa Kalou - jerin tauraren Afirka da Bundesliga za ta yi kewarsu lokacin gasar cin kofin Afirka a Gabon. Sai dai wasunsu sun ba wa kulob-kulob dinsu fifiko a kan kasashensu.
Juyin biri na babban dan zura kwallo
Ba abin mamaki ba ne da aka sa Pierre-Emerick Aubameyang, dan shekaru 27, cikin tawagar kasar Gabon a gasar cin kofin Afirka ta 2017 (AFCON). An bari ya tafi gasar ta AFCON a lokacin da Borussia Dortmund ke matukar bukatarsa. Dan wasan ya ci kwallo 16 a wasanni 15 na kakar Bundesliga ta bana. Da wahala a san inda Borussia Dortmund za ta kasance ba tare da shi ba.
Aro daga Tottenham
Dan kasar Aljeriya Nabil Bentaleb ya shiga kulob din Bundesliga ta Schalke a matsayin aro na tsawon kakar wasa a watan Agustan 2016. Tun isowarsa, dan shekaru 22, kuma dan wasan tsakiya ya ci kwallaye biyar a wasanni 21. Schalke na da zabin sayen dan wasan, wanda har yanzu yake karkashin wata kwangila da kulob din Tottenham Hotspur.
Barka da zuwa Bundesliga
Bernard Tekpetey dan shekaru 19, matashi ne mai hazaka da ya shiga Schalke daga kulob din kasar Ghana wato Unistar Soccer Academy a watan Janairun 2016. A mako na 15 na kakar Bundesliga ta bana ya wa Schalke wasansa na farko a Bundesliga, bayan ya fara dandana wasan kwallon kafa na kasa da kasa a gasar Europa League a karshen watan Nuwamba.
Fifita kasa a kan kulob
Haifaffen kasar Faransa, Marcel Tisserand mai tsaron baya na Kwango ne da ke wasa a kulob din Ingolstadt. Tisserand, wanda ya bayyana a wasanni 13 tun bayan shigowarsa Bundesliga daga kulob din AS Monaco a lokacin bazara, za a yi kewarsa a kulob dinsa da ke gwagwarmaya a Jamus. Ingolstadt ta tafi hutun lokacin sanyin hunturu tana a matsayi na 17 a jerin Bundesliga.
Club over country
Marvin Matip dan shekaru 31 an haifeshi ne a Bochum, mahaifinsa dan Kamaru, mahaifiyarsa 'yar Jamus. Yana iya wa Jamus ko Kamaru wasa, amma ya zabi Kamaru. Sai dai kyaften din na Ingolstadt ya zabi ba da fifiko ga kulob dinsa da ke fuskantar barazanar komawa mataki na kasa, kamar takwarorinsa 'yan wasan Kamaru guda shida ciki har da dan uwansa da ke wa Liverpool wasa.
Kai hari na mai tsaron baya
Abdul Rahman Baba (dama) dan Ghana da aka ba wa Schalke aronsa daga kulob din da ke kan gaba a Premier League wato Chelsea. Ya ce ya zabi shirin aron bayan sabon kocin Chelsea Antonio Conte ya ce ba zai samu damar bugawa a can ba saboda salon wasansa na tsaron baya ana kai hari. Dan shekaru 22 ya buga wa Ghana dukkan wasanninta a gasar Africa Cup a Equatorial Guinea a 2015.
An AFCON veteran
Yatabare dan Mali ne da yanzu yake wa Werder Bremen wasa a tsakiya. Dan shekaru 27 ya wakilci kasarsa a gasar AFCON ta 2015, ya ci wa tawagarsa kwallon farko a gasar inda suka yi canjaras da ci 1–1 da Kamaru. Kulob dinsa ta Werder, da yanzu ke a matsayi na 15 a Bundesliga, tabbas za ta yi amfani da taimakonsa a gwagwarmayar tsallake siradi.
'Yar sararawa daga gwagwarmaya
Änis Ben-Hatira dan shekaru 28, haifaffen Berlin da ke wa Tunisiya wasan kwallon kafa, yana wa kulob din Darmstadt wasa a tsakiya. Kasarsa na cikin rukuni daya mai karfi tare da Aljeriya, Zimbabuwe da kuma Senegal. Ya san irin abinda Tunisiya ke sa rai daga gareshi, amma a Jamus kulob dinsa na matukar bukatar dukkan taimako da za su samu a gwagwarmayar tsallake siradi.
Bangaren tarihin nasarorin kulob din Hertha
Ta kasance shekara mai ban mamaki a gasar Bundesliga. Bayern Munich na kan gaba, sabon shiga RB Leipzig a matsayi na biyu, yayinda Hertha Berlin da Salomon Kalou ke wa wasa ke a matsayi na uku. Kalou dan shekaru 31, dan Cote d'Ivoire ne, da ke wasa a matsayin mai kai hari ga Hertha da kuma kungiyar kwallon kafar kasa ta Cote d'Ivoire. A kakar bana ya ci wa kulob dinsa kwallo biyar.
Soyayyar Schalke ta gaske
Dan wasan Bundesliga da Kamaru za ta iya yi ba tare da shi ba, shi ne Eric Maxim Choupo-Moting, haifaffen birnin Hamburg. Dan shekaru 27, da aka sanshi da kwazo da iya murza leda ya buga wa Kamaru a gasar cin kofin duniya sau biyu. Sai dai jim kadan gabanin Schalke ta fara shirye-shiryen fara zagaye na biyu na Bundesliga, Choupo-Moting ya sanar cewa zai kaurace wa gasar Africa Cup.