Fararen hula sun hallaka a wani ruwan Bama-bamai Afganistan
March 25, 2019Talla
Akalla fararen hula 13 sun hallaka ciki har da kankanan yara 10 a Afganistan sakamakon wani farmakin bama-bamai ta sama da sojan kasa da kasa suka kai a garin Kunduz da ke arewacin kasar. Tawagar MDD a kasar ta Afganistan MANUA ta ce goma daga cikin 13 da suka kwanta dama duk 'yan gida guda ne, sannan ta nuna alhini game da abin da ya auku. Baya ga rundunar sojan Kasar Afganistan Kasar Amirka na kai hare-hare ta sama ga mayakan kungiyar Taliban kai a kai.