1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 1,000 sun mutu a girgizar kasa

Abdul-raheem Hassan
June 22, 2022

Hukumomin jinya na cewa adadin mutanen da suka mutu zai iya haura 1,000 yayin da wasu 1,5000 ke kwance a gadajen asibiti sakamakon ibtila'in girgizar kasa mai karfin maki 6.1 a kudancin kasar da ke iyaka da Pakistan.

https://p.dw.com/p/4D4rl
Afganistan | girgizar kasa
Hoto: Bakhtar News Agency/AP/picture alliance

Jami'an agaji sun ce girgizar kasar ta rusa daruruwan gudaje a yankunan marasa galihu, an kuma yi gargadin bala'in ka iya shafar makwabtan kasashe kamar Iran da Pakistan.

Masu ayyukan ceto sun garzaya yankin da jirgin sama mai saukar ungulu don ba da taimako, amma da alama suna fuskantar tangarda sakamakon ficewar yawancin hukumomin agaji na kasa da kasa tun bayan da Taliban ta kafa gwamnati a shekarar 2020.

Wannan dai na zama babban gwaji ga gwamnatin Taliban bayan janyewar sojojin Amirka da suka mamaye kasar tun bayan harin 9 ga watan Satumban 2001 a mastayin daukar fansa.