Taliban za ta dawo da shari'ar musulunci
September 23, 2021Daya daga cikin shugabanin Kungiyar Taliban na Afghanistan, ya ce, ba makawa, za a ci gaba da aiwatar da hukuncin kisa da yanke hannun wadanda aka samu da aikata laifi bisa koyarwar shari'ar musulunci.
Mullah Nooruddin Turabi, ya kara da cewa, abin da za a rage, shi ne aiwatar da hukuncin a bainar jama'a kamar yadda Taliban tayi a can baya. Ya dai fadi hakan ne a yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na AP, daga bisani ya yiwa kasashen duniya kashedi, kan su guji tsoma baki a sha'anin shugabancin Taliban, tun da a cewarsa, Taliban ba ta damu da yadda suke gudanar da ta su sha'anin mulkin ba.
Tun da Taliban ta kwace iko a farkon watan Augustan bana, da dama daga cikin 'yan kasar da sauran kasashen duniya suka soma baiyana fargaba kan yiyuwar dawo da dokoki masu tsauri da kungiyar ta mulki kasar da su a shekaru 1990 kafin a hambararr da gwamnatin.