1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Hari kan ma'aikatan gwamnati

February 9, 2021

Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatan gwamnati 5 ne suka mutu a wani tagwayen hare-hare a babban birnin Afghanistan daga cikin harin baya-bayan nan da aka kai wa fararen hula.

https://p.dw.com/p/3p7Vg
Afghanistan Kabul Bombenanschlag
Hoto: Rahmat Gul/AP/picture alliance

Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne dai suka bude wuta ga ma'aikatan Sashin Bunkasa Tattalin Arzikin Karkara da kuma Lardi na kasar da ke gabashin birnin Kabul. Jami'ai da masu kare hakkin bil-adama na kokawa kan yadda ake samun karuwar hare-haren a kullum a kasar, 

Jami'an gwamnati sun ce hare-haren da ake kaiwa na mayar da hankali ne kan cibiyoyin da ke birane kuma ke zuwa bayan tattaunawar zaman lafiya da aka tsawaita da mayakan Taliban da ke fadan neman iko tun a shekarar 2001, sai dai Kungiyar Taliban din ta ce ba ita ke da alhakin kai harin na wannan Talatar ba.