Taliban na kara karfin ikonta
August 8, 2021Talla
Wata sanarwa da majalisar dokokin gundumar ta Kundus ta fitar, ta nunar da cewa tuni 'yan Taliban din suka kwace iko da muhimman gine-ginen gwamnati, yayin da jami'an tsaro suka janye daga hanyar da ke zuwa filin jiragen sama na gundumar. Cikin 'yan kwanakin da suka gabata dai, Taliban din ta kwace iko da manyan biranen gundumomi uku. Tun bayan sanar da janyewar dakarun Amirka da na kungiyar tsaro ta NATO daga Afghansitan zuwa karshen wannan wata na Agusta da muke ciki, kungiyar Taliban ke kara fadada ikonta a yankuna da dama tare da kai munanan hare-hare.