Sharhunan jaridun Jamus kan Afirka
April 7, 2023Jaridar Der Tagesspiegel ta wallafa labarin da ya mayar da hankali ne kan kasar Mali musamman ma gwamnatin mulkin sojan kasar wadda jaridar ta ce, ta gaza share fage na mika mulki ga gwamnatin da za ta kasance kan doro na demokradiyya. Tun bayan da soji suka yi mulki shekaru kusan 3 da suka gabata, ake ta kokarin samar da sauyi a kasar da nufin mayar da mulki hannun farar hula. Guda daga cikin batutuwan da ake kokarin yi shi ne, amincewa da sabon kundin tsarin mulki a wata kuri'ar raba gardama da aka tsara yi, ya zuwa yanzu ba a samu nasarar yin hakan ba, bayan da sojojin suka dage shi bisa uzurin da suka bayar na cewa, hukumar zaben kasar na bukatar lokaci don kimtsawa da kuma ilimantar da jama'a kan abin da daftarin kundin tsarin mulkin ya kunsa.
Ita kuwa Jaridar Die Zeit sharhinta ya mayar da hanaklai kan abin da ta kira kokarin da jam'iyyar ANC da ke mulki a Afrika ta Kudu ke yi wajen ganin ta tattauna kan kalubalen da take fuskanta a yayin wata ziyara da jiga-jigan jam'iyyar za su kai fadar mulkin Rasha ta Kremlin nan gaba kadan. Jaridar ta ce, baya ga zantawa kan halin da ANC din ke ciki wanda za a yi tsakanin mambobin da jam'iyya mai mulki a Rasha, bangarorin biyu za su tattauna kan sabon salo na mulkin mallaka a duniya. Har wa yau, za su kuma zanta kan irin alakar da ke akwai tsakanin Rasha da kuma Afrika ta Kudu wadda ta samo asali tun lokacin yakin cacar baka.
Sai dai musa sanya idanu kan irin dangantakar da ke akwai tsakanin bangarorin biyu na ganin ziyarar, wani yunkuri na karar yaukaka dangantaka tsakanin kasashen da kuma samar da wani yanayi na kara angizon Rasha a kasar. Wasu na yi wa lamarin kallo na share fage na halartar Shugaba Vladimir Putin, taron kasashen da ke cikin kungiyar nan ta BRICS wanda za a yi a watan Agustan da ke tafe, taron da wasu ke son ganin an yi amfani da shi wajen kama Putin din don mika shi ga Kotun ICC da nufin fuskantar laifukan yaki.
Jaridar Die Tageszeitung ta wallafa labari mai taken ''karuwar sacewa da kuma kisan yara 'yan makaranta da ya tada hankalin al'umma a kasar Zambiya''. Jaridar ta ce, yanayin da al'umma ke ciki a kasar ta Zambiya ya kara tada hankalin al'umma bayan da aka tsinci gawar wani yaro dan shekaru 7 da haihuwa wanda ya bace a kwanakin baya. Jaridar ta ce, alamu na nuna yaddda masu sace mutane wadanda ake zargin 'yan kungiyoyin asiri ne, ke amfani da dabaru iri-iri wajen sace mutane a kasar kuma hankalinsu ya fara karkata kan mata don a baya-bayan 'yan sanda sun sanar da bacewar mata akalla 10, batun da suka bayyana a matsayin lamari mai tada hankali.
Su ma dai 'yan siyasa a kasar musamman ma na jam'iyyar adawar nan ta Patriotic Front ko kuma PF a takaice, nuna damuwa suka yi game da wannan lamari wanda suka ce matsin tattalin arzikin da aka shiga a kasar na da alaka da batun sace-sacen mutanen da ake yi, domin kuwa a wasu lokutan masu sace mutanen kan nemi kudin fansa daga hannun dangin wanda aka sace. Sun kuma nemi mahukuntan kasar da su gaggauta yi wa tufkar hanci.