Sharhunan Jaridun Jamus kan Afirka
May 8, 2020Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce matakan da gwamnatocin nahiyar Afirka ke dauka don dakile yaduwar cutar coronavirus, na yin mummunan tasiri ga rayuwar al'umma. Ta ce a karshen watan Afrilu Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yi gargadin cewa idan ba a gaggauta daukar sahihan matakai ba Afirka za ta fuskanci mummunar matsalar karancin abinci, musamman duba da cewa tun gabanin bullar annobar coronavirus din, mutane kimanin miliyan 821 ne ke fama matsalar yunwa, baya ga karin wasu miliyan 135 da ke cikin matsananciyar yunwa.
Rawar da COVID-19 ta taka
Sannan sakamakon matakan da ake dauka na yaki da cutar COVID-19, an samu karin mutane miliyan 130 da suka shiga jerin masu bukatar abin sakawa a bakin salati cikin gaggawa. Wadannan mutane dai, idan ba a tashi tsaye ba yunwar ka iya yin ajalinsu a kusan kasashe 36 a Afirka.
Wani abin da ke kara munin matsalar shi ne yadda coronavirus ta gurgunta tattalin arzikin kasashe masu karfin masana'antu, wadanda bisa al'ada ke bai wa takwarorinsu na Afirka tallafi. Rufe kan iyakoki na kasa da na sama da aka yi don hana cutar yaduwa, ya janyo babban koma-baya wajen jigilar kayan agaji da suka hadar da abinci da magunguna, har da ma katsewar harkokin kasuwanci a daukacin kasashen na Afirka. Matukar hakan ta ci gaba to akwai fargabar cewa yunwa za ta yi ajalin yawan mutane fiye da wadanda coronaviru din ta kashe.
Nakasu a harkokin wasanni
Wasannin motsa jiki ma dai sun fuskanci nakasu sakamakon cutar ta corona, a kan haka ne jaridar Berliner Zeitung ta yi sharhi tana mai cewa an dauki matakan ladabtarwa a kan dan wasan kungiyar Hertha Berlin kuma dan kasar Cote d'Ivoire Salomon Kalou bisa tabargazar da ya yi na fatali da dokokin yaki da cutar corona.
A wani faifayen bidiyo da ya wallafa a internet, dan wasan kwallon kafar ya yi ta yin musafaha da takwarorinsa, abin da ya saba da ka'idojin tsabta da kungiyar ta Hertha Berlin ta shimfida na yaki da yaduwar corona a tsakanin 'yan wasanta. Ya kuma nuna takardar ragin albashinsa. Wannan rashin biyayya da dan wasan ya yi ya keta ba ma kawai dokokin kungiyar ba, har ma da dokokin hukumar kula da wasannin lig-lig ta Jamus, wato DFL, inji jaridar. Yanzu haka dai kungiyar ta dakatar da shi, kuma babu masaniya kan cewa ko za ta sabunta kwantiraginsa da za ta kare a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa.
Za mu karkare da jaridar Der Tagesspiegel wadda ta labarto cewa gwamnatin Tarayyar Jamus za ta fadada aikin da dakarunta ke yi a kasar Mali mai fama da tashe-tashen hankulan 'yan Jihadi. Ta ce wannan mataki na zuwa ne daidai lokacin da Jamus ta rufe cibiyoyin bayar da horo ga sojojin Mali saboda fargabar coronavirus, ko da yake kawo yanzu ba a samu ko da soja guda na Jamus din da ya harbu da kwayar cutar ta corona a Mali ba. A cewar gwamnatin Jamus za ta karfafa aikin bai wa sojojin Mali horo a yakin da ake yi da 'yan ta'adda.