Sharhin Jaridun Jamus kan Afirka
May 15, 2020A labarinta mai taken "Tituna na cikin hadari- za a saki dubban fursunoni", jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta bayyana cewa a makonni masu zuwa ne shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ke shirin sakin fursunoni wajen dubu 19, daga cikin kimanin dubu 155 da ke garkame a gidajen yarin kasar. Hakan kuwa ba ya rasa nasaba da cutar coronavirus da ke ci gaba da yaduwa a cikin kasar. Sannu a hankali dai wannan annoba ta fara isa cikin gudajen kurkukun. Tuni dai aka tabbatar da cutar a jikin fursunoni 198.
'Yan adawa na adawa
Wannan mataki a cewar sanarwa fadar shugaban kasar, na nufin mayar da hankali wajen yaki da yaduwar COVID-19. A hannun guda kuma, an kafa dokar kulle ga al'ummr kasar sama da da miliyan 56 na tsawon makonni shida. Koda yake ana barinsu suna fita domin motsa jiki tsakanin karfe shida zuwa tara na safe da zuwa wajen likita ko kuma sayen kayan abinci. Sai dai 'yan adawar kasar ba sa farin ciki da shirin sakin fursunonin. Afirka ta Kudun dai na daya daga cikin kasashen da aka fi aikata miyagun laifuka a duniya. A kalla mutane 58 ake kashewa a kowace rana, a yayin da ake yin fyade da wasu nau'o'in cin zarafin mata sama da 144 a kasar.
Ita kuwa jaridar Neues Deutschland sharhi ta rubuta dangane da halin da yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ke ciki. Jaridar ta ce da yawa daga cikin al'ummar wannan yankin na fama da talauci da yakin basasa, sai kuma ga cutar corona ta kunno kai a wannan yanayi. Sannu a hankali dai yawan wadanda ke dauke da cutar coronavirus din, na kara yawa a kasashen Afirka da ke yankin Kudu da Sahara. Sai dai kuma wannan doka ta kulle da kasashen ke sawa, ita ma tana da tata illa babba, alal misali a Kwango. Ka zauna a gida saboda corona? Wannan ba abu ne mai yiwuwa ba a cewar Sifa Adisa. Tana sayer da kayan marmari kamar ayaba da lemuo da abarba a kullunm a kasuwa, domin ta samu kudin haya da na sayawa 'ya'yanta biyu abinci. Duk da cewar tana fargaba dangane da wannan cuta, ya zama wajibi ta fita a kowace rana.
Cutar na habaka a Afirka
Mutane da yawa na cikin irin wannan yanayi na Sifa, a dukkan kasashen Afirka. Tun a farkon watan Maris ne dai cutar corona ta bulla a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. 'Yan kasuwa da 'yan siyasa da jami'an aikin agaji daga ketare ne suka shigo musu da ita daga tafiye tafiyensu. Tun bayan nan cutar sai kara habaka take yi, inda yanzu ake da mutane sama da 1000 da ke jinya, kana 44 sun rasa rayukansu. Kamar sauran kasashen Afirka, Kwangon ta rufe kan iyakokinta da makarantu. Kana ba a yarda a bude wuraren kasuwanci ko kuma shakatawa ba.
"Maganin sihiri daga Madagaska" da haka jaridar Die Tageszeitung ta bude wani labari da ta wallafa kan maganin gargajiyar da ya samo asali daga Madagaska, wanda ke karfafa garkuwar jiki domin taimakawa yaki da cutar COVID-19. Kasashen Afirka da dama, sun yi maraba da wannan magani. Sai dai Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ta nuna shakku dangane da sahihancinsa.
Kowa zai samu maganin
Shin ko Afirka ta gano makamin sirri na yakar COVID-19? COVID Organics ko kuma CVO a takaice daga Madagaska, yanzu shi ne ake tabka mahawara a kai. Tun bayan da shugaba Andry Rajoelina ya kwankwadi ruwan maganin a gaban kamarori na talabijin a watan Afrilu, tare da yin alkawarin dukkan al'ummar tsibirin miliyan 20 za su wadatu da maganin, kasashen Afirka suka shiga fafutukar samun sa. Tuni dai jagoran da ya binciki samo maganin ya nunar da cewar, ba ya warkar da kowace cuta, amma zai karfafa garkuwar jikin dan Adam.