1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka a jaridun Jamus 18.09.20

Mohammad Nasiru Awal AMA
September 18, 2020

Takaddamar siyasar Mali bayan juyin mulki da takarar Ngozi Okonjo-Iweala a kungiyar cinikaiya ta duniya sun ja hankalin jaridun Jamus.

https://p.dw.com/p/3igFB
Ghana ECOWAS | Assimi Goita
Assimi Goita Shugaban kwamitin soja na CNSP da ya jagoranci juyin mulki a MaliHoto: AFP/N. Dennis

Za mu fara da jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka kasar Mali tana mai cewa har yanzu tsugune ba ta kare ba a Mali, bayan da shugabannin sojojin da suka yi juyin mulki suka ba wa kansu muhimman mukamai a gwamnatin rikon kwarya da za ta jagoranci kasar tsawon wata 18. Jaridar ta ce an cimma matsaya a tattaunawar da aka kammala a karshen mako game da sabuwar alkiblar da za a dora kasar, amma kuma sabuwar takaddama ta kunno kai, domin babbar kungiyar 'yan adawa ta M5 da boren da ta jagoranta daga watan Yuni zuwa Agusta ya kai ga kifar da gwamnatin Shugaba Ibrahim Boubacar Keita, ta yi fatali da sakamakon tattaunawar tana mai cewa sojojin sun tanadar wa kansu muhimman mukamai kamar na shugaban gwamnatin rikon kwarya da mukaddashinsa, sannan shugaban ne zai nada firaminista da za su jagoranci kasar tsawon shekara daya da rabi, su shirya zabe amma ba za su tsaya takara ba. Sai dai baya ga turjiya a cikin gida, sojojin kuma na fuskantar sabbin takunkuman kungiyar ECOWAS da a taron da ta yi a farkon wannan mako a kasar Ghana ta sake jaddada bukatar a mika wa farar hula mulki bayan shekara guda. 

Annobar corona na barazanar durkusa kasashen Afirka Annobar corona na barazanar durkusar da wasu kasashen Afirka da ke fama dinbim bashi inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung. Ta ce ko da yake yawan wadanda cutar ta yi ajalinsu a Afirka ko kusa ba su kai yadda aka yi hasashe ba, amma tattalin arzikin kasashen nahiyar ya shiga mawuyacin hali sakamakon annobar ta corona, farashin danyun kaya ya fadi kasa sannan kasashe da dama sun sanya dokar kulle, abin da ya janyo karancin kudaden shiga. Jaridar ta ruwaito cibiyoyin nazarin tattalin arzikin kasa irinsu Fitch na cewa basussukan da ke kan kasashen Afirka na karuwa cikin sauri fiye da na sauran kasashe masu tasowa. A wasu kasashen Afirka na Kudu da Sahara mizanin bashin ya kai makura ta yadda gaza biyan bashin ke kara zama abu mai yiwuwa. Jaridar ta ce daidai lokacin da basussukan ke karuwa, tattalin arzikin kasashen na kara shiga wani hali ga kuma barazanar da ake fuskanta ta mace-macen daruruwa dubbai na mutane saboda dalilai na yunwa da cututtuka.Tun bayan bulla corona hukumomin kudi na duniya irin su Asusun Ba da Lamuni sun kaddamar da gagarumin shirin tallafa wa Afirka cikin har da yafe wani kaso na bashi abin da masana ke cewa zai dan rage radadin wahalar da nahiyar ka iya shiga.

Afrika Senegal Coronavirus Pasteur Institute in Dakar
Wasu daga cikin ma'aikatan cibiyar binciken kwayoyin cututtuka a Dakar SenegalHoto: Getty Images/AFP/Seyllou

Takarar Ngozi Okonjo-Iweala na sin canja harkokin ciniki na duniya  A karshe sai jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan takarar neman shugabancin kungiyar cinikaiya ta duniya da tsohuwar ministar kudin tarayyar Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala ke yi. Jaridar ta ce 'yar Najeriya da ke son canja harkokin ciniki na duniya, shekaru bakwai Ngozi Okonjo-Iweala ta yi a kan mukamin ministar kudin Najeriya, kasar da ta yi kaurin suna wajen cin hanci da rashawa. A cikin wasu littattafai biyu da ta wallafa Okonjo-Iweala ta yi kokarin fito da matsalar siyasa a Najeriya, ta kuma nuna yadda ta yi bakin jini wajen masu fada a ji saboda yadda take yaki da cin hanci da rashawa. Jaridar ta ce a tsakanin mutum takwas da ke neman mukamin na shugaban kungiyar cinikaiya ta duniya, Okonjo-Iweala na gabansu. Ta kuduri aniyar canja fasalin kungiyar don kara yawan taimakon raya kasa a kasashe masu tasowa a kuma kawo karshen rashin daidaito da ke akwai a harkokin cinikaiya a duniya.

Nigeria Finanzminister Ngozi Okonjo-Iweala
Ngozi Okonjo-Iweala yar takarar shugabancin hukumar cinikayya ta duniyaHoto: NICHOLAS KAMM/AFP/Getty Images
Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani