Sharhunan Jaridun Jamus kan Nahiyar Afirka
March 31, 2023Jaridar Die Tageszeitung cikin sharhinta mai taken ''Wata sabuwar manufa a kasashen ketare a Afirka'' Jaridar ta ce, Turai na da sabon aiki soji a Afirka a yankin Sahel inda take da burin kara karfafa tsaro domin yaki da masu jihadi.Tuni gwamnatin tarrayar Jamus ta ba da hadin kai ga aikin wacce za ta aike da sojoji guda sittin domin isa a tawaga ta hadin gwiwar sojoji na Tarrayar Turai a Nijar, domin taimaka wa wajen yakar kungiyoyin 'yan ta’adda masu dauke da makamai amma gudanar da aiki zai kasance cikin ka'idojin kare hakkin bil'Adama da dokokin jin kai na kasa da kasa.
Yaki da ta'addanci a yankin Sahel
Tawagar horar da sojoji ta EU EUTM wacce a can baya ke kasar Mali da zama amma aka mayar da ita zuwa Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a Malin wadanda ke samun goyon bayan Rasha, na tattare kuma da dakarun Faransa na rundunar Barkhan da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya MINUSMA, inda Jamus take da sojoji kusan ɗari.
Sabanin Mali, ana kallon Nijar a matsayin abin koyi na samun nasarar hadin gwiwar sojojin kasashen yamma, kamar yadda Gidauniyar Konrad-Adenauer ta yi nazari a baya-bayan nan. Wa’aadin sojojin na Jamus a cikin EUMPM Niger, zai kamnmala karshen watan Mayu na shekara ta 2024
Kyamar 'yan gudun hijira
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta sharhin mai taken ''Aljeriya na korar baki da a karshe ke makalewa cikin hamada'' Aljeriya na korar dubun dubatar mutane a kowace shekara abin da ya saba wa dokokin kasa da kasa. Tun daga farkon shekarar 2023 kadai, mutane 10,000 ne suka rasa rayukansu a cikin hamada, a tsakanin Janairu zuwa karshen Maris na 2023 Hukumomin Aljeriya, sun kori baki sama da 10,200 'yan gudun hijira da bakin haure a bakin iyaka wadanda ake bari cikin hamada Nijar a cewar wata kungiyar faffutuka ta Alarme Phone.
Haka jaridar ta ce, Kungiyar Medecin Sans Frontiere ta yi kira ga kungiyar kasahen yankin yammacin Afirka da ta gagauta sanar da hanyoyin ceton mutanen da suka makale a garin Assamaka da ke a tsakanin Nijar da Aljeriya.
A cikin watan Fabrairu, shugaban Tunisiya Kais Saied ya harzuka bakin haure da wata sanarwa mai cike da kalaman makirci na wariyar launin fata, abin da ya janyo aka rika kai wa 'yan cirani hari a duk fadin kasar, ko da yake an daɗe ana fuskantar wariyar launin fata da tashin hankali da cin zarafi a yankin arewacin Afirka na Magrib, amma abubuwan da suka faru a baya-bayan nan a Tunisiya da Aljeriya sun dauki wani sabon salo.
Adawa da mu'amalar jinsi daya a Yuganda
Ita kuwa jaridar Tagesspiele Labarin ta buga dangane da dokar mai tsauiri da 'yan majalisun dokoki a Yuganda suka amince da ita a kan 'yan Madigo da Luwadi, jaddada cewa duk wanda ya yi kakkausar suka ga dokar hana Luwadi, zai fuskanci fushin gwamnati. Kwamishinan Kare hakkokin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya Volker Türkya ya ce, ba daidai ba ne.
Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung taken sharhin da ta buga, ''Shugaba Kagame ya yi afuwa ga jagoran Hotel Ruwanda Paul Rusesabagina'' Rusesabagina wanda ya shafe kwanaki 939 a gidan yari a kasar Ruwanda, a makon jiya ne tsohon manajan Hotel kuma sananne daga fim din Hotel Rwanda aka sakeshi bayan afuwar shugaban Paul Kagame na Rwanda.Tun farko wata kotu ta sameshi da laifin ta'addanci wanda akansa aka yanke masa hukuncin zaman gidan jari na tsawon shekaru 25 kafin a yi masa afuwa.