Corona: Karancin riga-kafi a Afirka
July 29, 2021Talla
Matshidiso Rebecca Natalie Moeti ta ce an samu wannan ci gaba ne a nahiyar da ke da yawan al'umma biliyan daya da miliyan 300, sakamakon yadda ake samun karuwar rarraba allurar riga-kafin COVID-19. Sai dai ta shaidawa manema labarai cewa, kaso 10 cikin 100 na allurar da ake bukata domin yi wa kaso 30 cikin 100 na al'ummar Afirkan nan da karshen wannan shekara ta 2021 ne kadai suka isa nahiyar. A cewarta kawo yanzu allurar riga-kafin miliyan 82 ne kacal suka isa Afirka, cikin miliyan 820 da ake bukata. Ta kara da cewa an bar kasashen Afirka a baya wajen yin riga-kafin, ta yadda kaso biyu ne kacal cikin 100 aka yi wa allurar kawo yanzu.