1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Kwamitin Sulhu: Kujera ga kasashen Afirka

September 26, 2024

Shugabannin kasashen Afirka sun yi tarayya, wajen gabatar da bukatar tsagaita bude wuta a Gaza da kuma batun samar da kujerar din-din-din a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya bayyana domin a ji muryoyinsu.

https://p.dw.com/p/4l7t5
Amurka | New York | Taro | Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya | Karo na 79
Taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na AmurkaHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Taron zauren Majalisar Dinkin Duniyar na wannan shekarar ya zo da wani sabon salo dangane da irin furuce-furucen, wadanda shugabannin kasashen nahiyar Afirka suka gabatar cike da burin kawo sauyi cikin gaggawa. Kama daga sababbin jini kamar Bassirou Diomaye Faye na Senegal da mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima da suka halarci taron da galibi  shugabannin kasashe ne kadai ke hawa mambarin zauren majalisar, har zuwa Cyril Ramaposa da ke takun saka da gwamnatin Isra'ila. An dai taba alli kan bukatun kashin kai da suka shafi kasashen nahiyar Afirka har zuwa matsayin Afirka a yakin Gaza da kuma halin da ake ciki a Lebanon, kai har ma da wakilcin Afirka a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya kasance jigon kalaman shugaban kasar Saliyo Julius Maada Bio.

Holland | The Hague | Afirka ta Kudu | Kara | Gaza
Kotun hukunta laifukan yaki da ke birnin The Hague na kasar HollandHoto: Piroschka van de Wouw/REUTERS

Kalaman da Shugaba Cyril Ramaposa na Afirka ta Kudu ya jaddada a jawabinsa da ya gabatar a zauren majalisar. Dangane da batun yakin Gaza kuwa, shugaban Afrika ta Kudu ya yi jawabi da kakkausar murya ta la'akari da rawar da kasarsa ke takawa wajen kawo karshen yakin a daftarin da hukumomin Pretoria suka gabatar a kotun Kasa da Kasa ta Duniya da ke The Hague na kasar Holland. Sai dai ra'ayi ya bambanta tsakanin Ramaposa da takwaransa na Angola Joao Lourenco da ya ce, Isra'ila na da damar kare kanta daga duk wata barazana amma akwai bukatar kare fararen hula. Rashin hukunci da danniya da wariyar launin fata har ma da rashin adalci na neman jefe duniya cikin rudani a wannan karni da ya kamata ace an mayar da hankali wajen tabbatar ci gaban zaman lafiyar duniya, a cewar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniy Antonio Guterres. Rikice-rikice kama daga yakin basarar Sudan da na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da tasirin yakin Rasha da Ukraine a Afrika da kuma kalubalen da kungiyar ECOWAS ke fuskanta, na bukatar daukin kasashen duniya.