1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka ta Kudu za ta fara alurar rigakafin corona

Binta Aliyu Zurmi
February 1, 2021

Miliyan guda na allurar rigakafin corona na kamfanin AstraZeneca sun isa kasar Afirka ta Kudu da yammacin wannan rana ta Litinin.

https://p.dw.com/p/3ogvh
Südafrika Präsident Ramaphosa
Hoto: AFP

Shugaban kasar Cyril Ramaphosa da mataimakinsa gami da ministan lafiyar kasar Zweli Mkhile ne suka tarbi jirgin saman da ya kai alluran, inda suka nuna cewa sahun farko na wadanda za a fara yi wa rigakafin sune mutanen da ke aiki a fannin kiwon lafiya da tsofaffi kafin daga bisani a kai ga yiwa sauran al'umma.

Kasar Afirka ta Kudu dai ita ce a kan gaban kasashen da cutar corona ta fi yiwa barna a nahiyar Afirka, sama da mutum miliyan daya da dubu dari biyar ne cutar ta harba hakazalika ta yi sanadiyyar mutuwar sama da wasu dubu 44.

Afirka ta Kudu ta jima tana jiran samun rigakafin da zai isa al'ummar kasar da yawansu ya kai kusan miliyan 60. Yanzu haka suna jiran karin wasu rigakafin miliyan 12 wanda suka yi yarjejeniya da Hukumar Lafiya ta Duniya da kuma wasu daga kungiyar tarayar Afirka.